IQNA

An Bugawa ‘Yan Makaranta Barkonon Tsohuwa A Bahrain

23:05 - January 12, 2017
Lambar Labari: 3481127
Bangaren kasa d akasa, jami’an tsaron masarautar Bahrain sun harba wa dalioban makarantar sakandare barkonon tsohuwa jim kadan bayan kammala jarabawa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoton cewa, tashar Press TV ta ce mahukuntan Bahrain sun dauki wannan matakin ne sakamakon dokar hana taron mutane da suka wuce biyar.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkokon tsohuwa kan daliban wadanda suke fitowa daga makarantnsu bayan sun kammala rubutun jarabawa, inda suke da niyyar tafiya gidajen iyayensu.

Masarautar Bahrain a kowane lokaci tana cikin tsoron barkewar zanga-zangar al’ummar kasar, sakamakon kuncin da matsin da ta jefa su a ciki,saboda dalilai na siyasa da kuma banbancin mazhaba.

Wannan ne ya sanya masarautar ta kafa dokar cewa, ba a yarda mutane fiye da biyar su tari a wani wuri ba, domin kada su jawo wani gangami na bore ga wannan masarauta.

Da dama daga cikin al’ummar kasar Bahrain dai suna gudanar da taruka domin nuna goyon bayansu ga babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Kasim, wanda masarautar mlkin kama ta kasar ta sanar da janye izinin zama dan kasa a kansa, bisa hujjar cewa yana mara baya ga masu adawa da salon mulkin masarautar kasar.

Bahrain dai na daga cikin kasshen da turawn mulkin mallakar birtaniya suka kafa masarautu a cikinsu, inda suka mika ragamar tafiyar da lamurra ga iyalan gidan khalifa, wadanda suke mulkin kasar da karfin bindiga.

3561772


captcha