IQNA

Karuwar Kyamar Musulmi A Kasar Belgium

20:59 - January 13, 2017
Lambar Labari: 3481131
Bangaren kasa da kasa, an samu karuwar kyamar musulmi a kasar Belgium inda fiye da kashi 60 na mutanen kasar ke kallon musulmi a matsayin wata barazana.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, wata daya daga cikin manyan jaridun kasar Belgium ta gudanar da wani jin ra’ayin jama’a s kasar wanda ya nuna cewa kyamar musulmi ta karu matuka.

Bayanin jaridar y ace sakamakon jin ra’ayin da ta gudanar ya nuna cewa, fiye da kashi 60 cikin dari na mutanen kasar suna kallon musulmi a matsayin barazana a gare su, yayin da kashi 12 ke kallonsu a matsayin wani arzikina kasa.

Haka nan kuam jaridar ta ce kimanin kashi 28 na mutanen kasar bas u da wani ra’ayi kan yadda suke kallon kasantuwar musulmi a kasar.

A bangaren musulmi kuma da jaridar ta ji ra’ayinsu, kimanin kashi 71 na musulmin da ke kasar Belgium suna jin cewa mutanen kasar na kallonsu a matsayin ‘yan ta’adda ne, kuma suna zarguwa duk inda suka shiga suna jin cewa a haka a ake kallonsu.

Abin tuni a nan dais hi ne, a watannin da suka gabata ne kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da mummunar akidar nan ta kafirta al’umma irin su SIS, suka kaddamar da hare-hare a cikin birnin Brussels fadar mulkin kasar, wanda hakan ya kara jawo fushin al’ummar kasar a kan musulmi.

3562025


captcha