IQNA

An Kafa Gungun Kamfe Na Yaki Da Wariya Ga Mata Masu Hijabi A Landan

22:18 - January 14, 2017
Lambar Labari: 3481133
Bangaren kasa da kasa, wata mata musulma da ta fuskanci cin zarafi a kasar Birtaniya saboda hijabin da ta saka ta kafa wani gungu na yaki da irin wannan tabi’a

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «manchestereveningnews» cewa, Nahila Ashraf wata musulma ce ‘yar kasar Amurka da ta kafa kwamitin yaki da wariyar launin ko banbanncin addini a Washington ta isa kasar birtaniya domin halartar wani taro, amma ta fuskanci cin zarafi.

Wani mutum mai tsananin kyamar musulmi ya yi yin kalaman batunci a gare ta saboda ta saka hijabin mussulunci, amma wani dga cikin wadanda suke tare da ita ya buga wa ‘yan sanda waya, kafin ya iso mutumin ya tsere.

Ashraf ta ce wannan shi ne karon farko da ta taba ganin irin wannan cin zarafi a rayuwarta, domin kuwa koa akasar Amurka ba ataba nuna mata kyma ba a matsayinta na musulma mai saka hijabi sai a kasar Birtaniya birnin landan.

Wannan lamari ya sanya Ashraf kafa wani gungu na mata musulmi da ma wasu maza domin daukar matakan yaki da wannan mummunar akida ta kyamar mata masu saka hijabi da kuma cin zarafin da ake yi musu.

Wannan gungun ya kunshi mambobi 50 wadanda za su rika sanya ido da bin kadun duk wani lamarin irin idan ya farua kasar ta Birtaniya.

Jami’an tsaron kasar Birtaniya sun shiga gudanar da bincike kn lamarin, tare da yin kira ga ‘yan kasar da su taimaka domin kame mutumin da ya aikata hakan matukar suka samu bayani a kansa ko wurin da yake.

3562422


captcha