IQNA

An Bukaci A Hana Wani Mai Kin Jinin Muslunci Halartar Taron Rantsar Da Trump

23:54 - January 15, 2017
Lambar Labari: 3481136
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar musulmin kasar Amurka ta bukaci da a soke sunan wani malamin addinin kirista mai tsananin kiyayya da musulmi daga cikin sunayen mutanen da aka gayyata domin halartar taron rantsar da Trump.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, A cikin wani bayani da Nahad Awwad babban sakataren cibiyar musulmin Amurka ya karanta, ya bayyana cewa suna kira ne da a dauki wannan mataki, domin tabbatar wa al'ummar Amurka cewa Donald Trump bai amince da kyamar wani bangaren al'ummar Amurka saboda addininsu, domin kuwa a cewar bayanin, idan wannan mutum ya halarci taron a matsayin wanda aka gayyata, ya nuna cewa abin da yake daidai ne a hukumance.

Franklin Graham mutum ne da ke bayyana tsananin kiyayyarsa ga addinin muslunci da ma musulmi, inda a cikin shekara ta 2015 ya shelanta wani kamfe na kyamar msuulmi, tare da yin kira da a rufe dukkanin masallatai da cibiyoyi gami da makarantun msuulmia a kasar Amurka, saboda a cewarsa musulmi su ne 'yan ta'adda, kuma addininsu shi ne yake kira zuwa ga ta'addanci.

Haka nan kuma ya taka gagarumar rawa wajen yada kyamar musulmi a tsakanin al'ummar Amurka, musamman ma wadanda suke halartar majami'arsa ko kuma suke sauraren bayanansa.

A ranar 20 ga wannan wata ne na Janairu za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, yayin da wasu 'yan majalisa 10 na jam'iyyar Democrat suka haramta wa kansu halartar taron.


3562693


captcha