IQNA

Tashin Gobara A Cikin Wani Masallaci A Birnin Washington Na Amurka

23:56 - January 15, 2017
Lambar Labari: 3481137
Bangaren kasa da kasa, Wuta ta tashi a cikin wani masallaci da ke cikin birnin Washington na kasar Amurka, inda dukkanin kaddarorin da ke cikin masallacin suka kone kurmus, duk kuwa da cewa musumi sun yi iamnin cewa da gangan ne aka saka wutar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta CNN ta nakalto daga jami'an 'yan sanda na birnin Washington cewa, ba su da shakku a kan cewa abin da yafaru aiki ne na ganganci, amma ba su da wani dalili da za su iya tabbatar da hakan.

Babban jami'in 'yan sanda na yankin Stew Melett ya bayyana cewa, hakai wutar ta yi barna matuka, domin kuwa ta nkone masallacin da kuma cibiyar musulmi da ke hade da masallacin, amma sun damke wani mutum mai suna Ishaq Wine William dan shekaru 37, wanda aka same shi a kusa da wurina lokacin da abin ya faru, kuma an sha samunsa da hannu wajen aikata laifuka na cutar da jama'a, a kan haka yana amsa tambayoyia hannun 'yan sanda.

A nata bangaren babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta bukaci jami'an tsaro da su gudanar da bincike na hakika a kan wannan batu, domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin gurfanar da su.

Cibiyar ta kara da cewa, saboda yanayin da wurin yake ciki, an dakatar da dukkanin ayyuka a masallacin da kuma cibiyar da ke wurin har zuwa lokacin da za a kammala gyaransu.



3562743
 
captcha