IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci Gwamnatin Nigeria Ta Mutunta Doka Ta Saki Sheikh Zakzaky

21:59 - January 16, 2017
Lambar Labari: 3481138
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta bin umurnin babban kotun kasar na ta saki shugaban harkar Musulunci na kasar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da ake tsare da su.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, mai rikon mukamin babban daraktan kungiyar ta Amnesty International a NijeriyaMakmid Kamara ne ya yi wannan kiran inda ya ce a yau Litinin ne wa'adin kwanaki 45 da babban kotun ta Abuja ta ba wa gwamnatin Tarayyar kasar da ta sake Sheikh El-Zakzaky din yake cika, don haka ya zama wajibi ne gwamnatin ta sake shi, in kuwa ba haka ba, to hakan yana a matsayin yin karen tsaye ne ga doka.

Har ila yau kuma kungiyar Amnesty International din ta bukaci gwamnatin da ta saki saura 'yan kungiyar Harkar Musulunci din (IMN) da su ma aka kama su tare da shugaban na su kuma ake ci gaba da tsare su.

A ranar 2 ga watan Disambar bara (2016) ne alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja mai shari'a Gabriel Kolawole ya bukaci gwamnatin da sake Sheikh El-Zakzaky da matarsa Zeenat Ibrahim cikin kwanaki 45 da kuma biyansu diyyar Naira miliyan 50 saboda tsare su da aka yi ba tare da shari'a ba.

A watan Disamban shekara ta 2015 ne jami'an tsaron Nijeriya suka kama Sheikh El-Zakzaky a gidansa da ke Zariya bayan wani rikici da ya shiga tsakanin mabiyansa da sojojin Nijeriya a garin na Zaria, inda aka kashe daruruwa daga cikin mabiyan nasa.

3563307


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha