IQNA

Ana Tatatra Littafan Sheikhul Fitna A Kasar Masar

22:03 - January 16, 2017
Lambar Labari: 3481139
Bangaren klasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar tana tattara littafan Yusuf Qardawi wanda aka fi sani da malamin fitina.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alfajr cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta bayar da umarnin tattara littafan da suke dauke da akidu na masu tsatsauran ra’ayi a kasar.

Mahukunta alardin Suiz sun sunar da cewa sun samu nasarar gano wasu littafai kimanin 350 na masu tsatsauran ra’ayin kafirta musulmi.

Wannan mataki kuwa ya hada har da littafan malamin fitina da kuma wasu daga cikin littafan da aka rubuta da suke dauke da akidu masu matukar hadari a tsakanin al’ummar msuulmi.

A nasa banharen Ahmad karimah daya daga cikin malaman fikihu a cibiyar Azhar ya yi kakkausar suka dangane da yadda mahukuntan na Masar ba su hana shigar da littfan ‘yan salafiyya zuwa wasu lardunan kasar da suka hada da Iskandariya, Sinai da kuma Matruh.

Inda ya ce da dam adaga cikin littafan da ‘yan salafiyya suke shigowa da su a kasar suna dauke da irin wadannan akidu na kafirta sauran musulmi, wanda hakan ne ke kai matasan musulmi shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda da sunan jihadi a tafarkin sunna, suna kasha musulmi tare da tayar da bama-bamai sakamakon irin wannan akida ta salafiyyaci.

Daga cikin littafan da aka kame har da wadanda Sheikh Hassan Albanna ya rubuta wanda kuma shi ne wanda ya kafa kungiyar yan uwa musulmi a kasar, sai kuma littafan Yusuf Qardawi, wanda shi ma dan masar ne da ya tsere a halin yanzu yana zaune a gidan sarkin Qatar ya bayar da fatawoyin goyon bayan kungiyotin ‘yan ta’adda na duniya, inda yake bayyana abin da suke na kisan musulmi da mata da kanan yara da cewa jihadi ne.

3563213


captcha