IQNA

Kiristoci 14 Ne Suka Karbi Addinin Muslunci A Najeriya

23:26 - February 27, 2017
Lambar Labari: 3481267
Bangaren kasa da kasa, Kiristoci 14 ne suka karbi addinin muslunci a wani shiri na isar da sakon muslunci da ake gudanarwa a jahar Kwara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labara na Nigria bulletin ya bayar da rahoton cewa, a wani shiri da aka gudanar domin wayar da kan jama'a dangane da addinin muslunci mai taken ACADIP Nigeria a jahar Kwara, inda Yusuf Adepoyo ya gabatar da lacca, kiristoci 14 suka muslunta a wurin, da suka hada da wani babban malamin addinin kirista.

Rahoton ya ce a cikin watanni shida da suka gabata, kiristoci 316 ne suka muslunta sakamakon gudanar da wannan shiri, inda ake gabatar da jawabai masu gamsarwa a kan muslunci, da kuma karba tambayoyi na mabiya addinin kirista kan wasu abubuwan da suke da bukatar bayani a kansu dangane da muslunci.

Tarayyar Najeriwa wadda adadin mutanenta ya tasamma miliyan dari biyu, ita ce kasa mai yawan jama'a fiye da kowace kasa a cikin nahiyar Afirka, kamar yadda kuma a bangaren tattalin arziki tana a sahun gaba a kasashen da suka karfin tattalin arziki a nahiyar, domin kuwa ita ce kasar da ta fi kowace kasa a Afirka yawan danyen man fetur da iskar gas.

Najeriya ta hada mabiya addinai daban-daban da kabilu daban-daban, amma addinin muslunci shi ne addinin da ya fi yawan mabiya a Najeriya, kamar yadda kabilar Hausa fulani ita ce kabilar da tafi kowace kabila girmaa kasar.

3578749


captcha