IQNA

Wakilin Gambia A Gasar Kur'ani:

Tunani Ya Canja A Kan 'Yan Shi'a Bayan Da Na Halarci Gasar Kur'ani A Iran

23:39 - April 24, 2017
Lambar Labari: 3481435
Bangaren kasa da kasa, wakilin kasar Gambia a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya a Iran ya bayyana cewa tunaninsa ya canja matuka dangane da yadda ya dauki 'yan shi'a a baya.

Abdulaziz Ali Sila, wakilin kasar Gambia a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Iqna cewa, ya sauyi matuka a cikin tunaninsa dangane da yadda yake zaton zai samu kasar Iran.

Ya ce bisa ga irin abubuwan da ake gaya masa mabiya mazhabar shi'a ba su ayrda da kur'ani da aka saukar wa manzon Allah Muhammad (SAW) ba, kuma ya ginu a kan wannan tunanin a rayuwarsa, amma kuma yadda Iran take bayar da muhimamnci ga lamarin kur'ani ya sanya ya fara yin shakku a kan hakan.

Wannan makaranci ya ci gaba da cewa, a lokacin da ya zo Iran domin halartar gasar kur'ani, ya ga cewa kusan dukkanin mutanen da suka zo daga kasashe fiye da tamanin ba 'yan shi'a ba ne, kuma kur'anin da ake karantawa shi ne kur'ani da kowa ya yi iamni da shi, shi ne kuma makarantan Iraniyawa da na 'yan shi'a da suka zo daga kasashen larabawa suke karantawa suna hardacewa, sabanin abin da aka saba gaya musu.

Ya ce hakika wannan lamari ya masa tasiri matuka, musamman kuma ganin yadda aka girmama su duk kuwa da cewa 'yan Afirka ne, amma ba a nuna musu wani banbanci, har ma a wasu lokuta ana fifita su a kan fararen fata, inda ya ce bai taba ganin an yi masa haka a wasu kasashen da ba na shi'a ba.

Daga karshe ya yi kira ga dukkanin musulmi da su zamatsintsiya daya madaurinki daya, domin yada gaba a tsakanin musulmi shi ne babban abin da ya raunana musulmi a duniya, tare da bayyana cewa yanzu ya fahimci cewa 'yan shi'a musulmi kamar kowane musulmi, domin kuwa abin da yagani da idanunsa Kenan, alhali duk sauran maganganu ana gaya masa ne kawai.

3592894
captcha