Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na baffalonews cewa, taron ya gudane tare da halartar masana kimanin 60 da kuma manema labarai.
Lee Kapela masani ne kan harkokin sadarwa daga jami'ar New York wanda ya halarci wurin zaman taron, ya gabatar da jawabi da ke yin ishara da muhimmancin gudanar da irin wannan taro.
Masanin ya bayyana cewa a halin yanzu musulmi suna fuskantar matsaloli na zamantakewa a cikin kasashen turai da hakan ya hada da Amurka, wanda kuma manema labarai da kafofin yada labarai su ne ya kamata su taka rawa wajen wayar da kan mutane dangane da mummunar fahimtar da suke ita akan musulmi, wanda fahimta ce ta kure.
Haka nan kuma wasu daga cikin manema labarai da yawansu ya kai 40 da suka halarci wurin, sun nuna gamsuwarsu matuka da jawaban da aka yi, tare da shan alwashin daukar nauyin gudanar ad aikin wayar da kai ga jama'a domin samun fahimtar juna.
3592987