IQNA

Za A Saka Wani Shafi Mai Dauke Da Ayoyin Kur’ani A kasuwa A London

23:25 - April 25, 2017
Lambar Labari: 3481438
Bangaren kasa da kasa, za a nuna wani kur’ani mai tsarki da aka rrubuta akan shudiyar takarda a birnin London domin sayar da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na almisriyun cewa, a cikin wannan mako ne za a nuna wani dadadden kur’ani wanda aka rubuta da shudiyar takarda, wanda za a sayar da shi a birnin London.

Wannan kur’ani dai ya kunshi wani bangare na surorin kur’ani mai tsarki, wanda aka rubuta da rubutu mai launin ruwan zinari, wanda kuma ya jima a tsawons hekaru a birnin.

Ana sa ran kudin wanann kur’ani zai kai tsakanin dala dubu 128 ziwa dubu 192, wanda hakan zai zama shi ne kwafin kur’ani da kedauke da wasu surori da aka sayar da kudi mafi tsada a kasar ta Birtaniya.

Wanann na daga cikin muhimman abubuwa da musulmi suka fara a kasar, da nufin fito da matsayin kayan tarihi na addinin muslunci, inda kan saka kudade ga abubuwa da suka danganci tarihin muslunci da suke a kasar, wanda mutane sukan saya.

Wannan takardun kur’ani suna da alaka ne da birnin Kirwan daya daga cikin biranan tarihi na muslunci a kasar Tunisia.

3593167


captcha