IQNA

Dakarun Sa Kai A Iraki Sun Fara Farmakin “Muhammad Rasulullah” A Mausul

23:27 - April 25, 2017
Lambar Labari: 3481439
Bangaren kasa da kasa, dakarun sa kai na kasar Iraki sun fara kaddamar da wani farmaki mai taken Muhammad rasulullah a Mausul.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga alalam cewa, Abu Mahdi Muhandis kwamandan dakarun sa kai nan a kasar Iraki ya sanar da fara kaddamar da wannan maki da nufi kammala tsarkake bangaren hagu na kudancin mausul daga ‘yan ta’addan takfiriyya na ISIS.

Wanna farmaki dai yana da matukar muhimancin domin kammala tsarkake sauran yankin da ya rage a hannun ‘yan ta’addan wahabiya na ISIS a gefen birnin Mausul.

Bayanin yace akwai wasu unguwanni da suka rage a hannun ‘yan ta’addana cikin tsohon garin Mausul a yammacin birnin, wdanda aka killace su, amma ana taka tsatsan kasantuwar ‘yan ta’addan suna garkuwa da fararen hula a cikin wadannan unguwanni.

Haka nan kuma wasu kwararru a kan gano ababe masu fashewa suna tafiya tare da wadannan dakaru, kasantuwar ‘yan ta’addan sna binzne nakiyoyi a dukkanin wuraren da aka fatattake su.

3593150


captcha