IQNA

Wani Dan kasar Aljeriya Ya Zo Na Daya A gasar Makafi Ta Duniya

23:50 - April 26, 2017
Lambar Labari: 3481440
Bangaren kasa da kasa, wani dan kasar aljeriya ya zo a matsayi na daya agasar duniya ta makafi da aka gudanar a Iran.

Kamfanin dilalncin lbaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a bangarorin makafi da kuma dalibai saui kuma mata, da kuma bangaren gasar kamar yadda aka sana tsawon shekaru.

Bayanin ya ce Abdullah Muhammadnajad sdan kasar Iran shi ne ya zo na biyu a wannangasa ta makafi, kamar yadda Hussain Shalal daga kasar Iraki ya zo na uku.

Wannan karon dai shi ne karo na farko da ake gudanar da gasar a bangarori daban-daban sabanin yadda aka saba gudanar da ita shekaru fiye da talatin da suka gabata, wanda lamarin ya kayatar matuka.

Da dama daga cikin wadanda suka halarci wannan gasa sun bayyana cewa ba abu ne mai sauki a iya gudanar da gasa a bangarori hudu a lokaci guda ba, domin kuwa kowan ebangare na bukatar kulawa ta musamman.

Daga karshe an bayar da kyutuka na musamman ga dukkanin wadanda suka kwazo a wannan gasa.

3593474

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha