Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Irna cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Kasimi ya fadi a yau cewa, an kirayi jakadan na kasar Pakistan domin nuna rashin gamsuwa da yadda Pakistan take gudanar da tsaro a kan iyakokinta da Iran, wanda hakan ne ya bai wa wasu 'yan ta'adda daga cikin kasar ta Pakistan damar kai hari a kan jami'an tsaro Iran a kan iyaka, tare da kashe 10 daga cikinsu.
Kasimi ya ce 'yan ta'addan sun yin harbi ne a kan jami'an tsaron Iran daga cikin kasar Pakistan, kuma bayan kashe jami'an na Iran sun shige a cikin kasar ta Pakistan, a kan Iran na jiran ganin pakistan ta dauki matakin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, tare da zartar musu da hukuncin da ya dace da su.
A nasa bangaren jakadan Pakistan a Iran ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma al'ummar Iran, tare da nuna rashin jin dadi kan abin da ya faru, kamar yadda ya yi alkawalin mika sakon ma'aikatar harkokin wajen Iran ga gwamnatin kasarsa.