IQNA

Wani Makarancin Kur'ani Ya Rasu Yana Karatu A Indonesia

22:03 - April 28, 2017
Lambar Labari: 3481447
Bangaren kasa da kasa, Ja'afar Abdulrahman fitaccen makarancin kur'ani mai tsarki ya rasu rasu yana cikin karatun surat mulk.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Astro Awani cewa, Ja'afar Abdulrahman makarancin kur'ani ne da ya yi suna matuka akasar Indonesia, kamar yadda kuma shi malami ne mai koyar da karatun kur'ani mai tsarkia kasar.

Wannan malami ya rasu ne a daidai lokacin da yake karanta wata ayau a ciki karatun wata aya da take magana a kan mutuwa da rayuwa da Allah ya halitta su domin ya jarraba 'yan adam domin ganin wanda zai fi kyautata aiki.

Rasuwan wannan malami dai a cikin wannan yanayi ta yi babban tasiria cikin zukatan mutane da dama a kasar ta Indonesia dam duniyar musulmi, musamman ganin yadda labarin rasuwar tasa ya watsu a cikin kankanin lokaci ta hanyoyin sadarwa.

Abdulrahman dai yana da almajirai da dama da suka yi karatun kur'ani a wurinsa, wadanda sukan gabatar da karatun kur'ani a taruka da daman a addini a kasar.

3593471







Wani Makarancin Kur'ani Ya Rasu Yana Karatu A Indonesia


captcha