IQNA

Kiran Malamai A Birtaniya Ga Masarautar Bahrain

23:39 - April 29, 2017
Lambar Labari: 3481448
Bangaren kasa da kasa, fiye da malaman addini 80 ne na kasar Birtaniya suka bukaci masarautar Bahrain da ta dakatar da batn hukunta Ayatollah Sheikh Isa Kasim.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin alalam cewa, fiye da malaman addini 80 ne na kasar Birtaniya suka bukaci masarautar Bahrain da ta dakatar da batn hukunta Ayatollah Sheikh Isa Kasim babban malmi mafi girma a kasar.

Bayanin ya ce aiwatar da duk wata shari’a a kan babban malamin irin Ayatollah Isa Kasim na tattare da hadari, domin kuwa shi mutum ne da ake girmama shia duniya, kuma yake da mabiya a koina a cikin fadin duniya.

Daga karshe malaman sun bukaci masarautar al khalifa da ta sake yin nazari ta dakatar da duk wani batun cewa za ta hukunta shi saboda dalilai na siyasa.

3594264


captcha