IQNA

Baje Kolin Kaya Domin Taimaka Ma Mutanen Somalia A Canada

23:45 - April 29, 2017
Lambar Labari: 3481450
Bangaren kasa da kasa, a masallacin Al-iman da ke garin Victoria a Canada za a gudanar da wani baje kolin kayan abinci domin taimaka ma mutanen Somalia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «timescolonist» cewa, za a fara gudanar da wannan taron ne da misalign karfe 16 na yammacin gobe, tare da halartar Liza Helpez magajiyar garin.

Isma’ila Muhammd Nur Nur shi ne limamamin masallacin Iman, ya ce a wurin za a gabatar da jawabai a kan halin da jama’a suke ciki a kasar ta Somalia, da kuma yin kira da a taimaka musu ta hanyoyin da suka sawaka.

Daga cikin mutanen da za su halarci wurin har da ‘yan kasar ta Somalia da kuma wasu jami’an gwamnati gami da musulmi da kuma wasu kungiyoyin da ke taimaka ma jama’a musamman marassa galihu.

Kasar Somalia dai na fama da matsaloli, inda ksan mutane miliyan 6.2 wato kimanin rabin mutanen da ke rayuwa a cikin kasar suke bukatar taimako na abinci da kayan masarufi na rayuwa.

Matsalolin da suka hada da yaki da kuma fari su ne sanadinfadawar jama’a cikin mawuyacin hali a kasar Somalia, wanda kuma taimakon da kasashen duniya ke bayarwa baya wadarwa.

Tun a cikin shekara ta 1991 aka fara yakin basasa a kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da tserewar wasu da dama.

3594001


captcha