IQNA

Cin Abincin Buda Baki Tare Da Musulmi Da Kiristoci A Masar

23:57 - June 24, 2017
Lambar Labari: 3481638
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslucni tare da mabiya addinin kirista a kasar sukan ci abincin buda baki tare domin kara dankon dankantaka a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Egyptian Streets cewa, a kowace shekara al’ummar kasar Masar musulmi da kiristoci suna da al’adar yin buda baki tare tsawon daruruwan shekaru.

Da dama daga cikin mabiya addinion kirista a kasar masar wadanda ‘yan kabilar Kibdawa ne, sukan gayyaci musulmi zuwa gidajensua lokacin buda baki, inda sukan shirya abinci wanda musulmi suke ci domin yin buda baki.

Kamar yadda kuma musulmin sukan gayyaci kiristoci zuwa gijaensu a lokacin azumin watan Ramadan domin buda baki ko cin abincin dare, ko kuma a wurare na taruka da musulmi kan shirya na buda baki a kan gayyaci kiristoci da malamansu, wanda hakan ya zama jiki ga al’ummar Masar.

A cikin lokutan baya-bayan nan dangantaka tsakanin musulmi da kibdawa ta yi sanyi, sakamakon hare-haren ta’addancin da masu dauke da akidartakfiriyya suke kaiwa kan majami’oin kiristci a kasar ta Masar, amma duk da haka malamai daga dukkanin bangarorin biyu suna yin kokarin ganin wannan kyakkyawan aiki ya ci gaba.

3612935


captcha