IQNA

Hotunan Sallar Idi Daga Birnin Karbala Mai Alfarma

20:02 - June 26, 2017
Lambar Labari: 3481644
Bangaren kasa da kasa,a yau ne aka gudanar da sallar idi a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki da tare da halartar dubban daruruwan jama’a a hubbarorion Imam Hussain (AS) da Abbas (AS).

Kamfanin dillancin labaran Nun ya habarta cewa, an gudanar da taron ne tare da halartar mutanen birnin da kuma baki daga sassa daban-daban na kasar masu ziyara da kuma ‘yan kasashen ketare.

A jiya ne dai babban malamin addini na kasar ta Iraki Ayatollah sayyid Sistani ya sanar da yau Litinin a matsayin ranar farko ta watan Shawwal na shekarar 1438, wanda za a gudanar da sallar idi.

A cikin matanin farisancin da ya zo a kan wanann batu, an yi ishara da cewa saboda rashin ganin jaririn watan shawwal a ranar Asabar hakan ya sanya ranar lahadi ta zama cikon watan Ramadana yankunan da ba a gani ba.

A can kasar Lebanon ma Ayatollah Abdul Amir Qabaln ya jagorancin sallar idi a yau, bayan da ya bayyana jiya Lahadi a matsayin cikon watan Ramadan mai alfarma.

3613484


captcha