Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Almisriyun cewa, an mutumin da aka nuna hotonsa sanye da kayan jami’an tsaro yana karatun kur’anun a gaban watya majami’a soja ne a kasar Masar.
Wannan faifan bidiyo ya dauki hankali mutane matuka musamman ganin cewa wannan mutum musulmi ne kuma yana gadin majami’a ta mabiya addinin kirista domin tabbatar da ya basu kariya domin kada a cutar da su, kuma hakan bai hana shi yin nasa addinin ba a lokaci guda.
Mai gabatar da shirin talabijin da nuna wannan faifan bidiyo ya bayyana cewa, hakika wannana bin da aka gani ya tabbatar da cewa al’ummar Masar basu da wata matsala a tsakaninsu, yan ta’adda ne suke neman haifar da matsala domin rarraba kan al’ummar kasar da sunan addini.
Kasar Masar ta fuskanci matsalolin hare-haren masu dauke da akidar wahabiyanci da ke kasha jama’a da sunan jihadi, inda kiristoci da majami’unsu bas u sha ba daga hare-haren ‘yan ta’adda