IQNA

Jagora A Lokacin Ganawa Da Jami'ai Da Kuma Jakadun Kasashe:

Fito Na Fito Da Yahudawan sahyuniya Wajibi Ne A kan Dukkanin Musulmi

16:36 - June 27, 2017
Lambar Labari: 3481647
Bangaren kasa da kasa, jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ce, a shari'ar addinin Musulunci, yin jihadi da yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila wajibi ne a kan dukkan musulmi a ko ina suke a duniya.

Kamfanin dillancin labaraniqna ya habarta cewa, Jagoran ya bayyana haka ne a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da jami'an gwamnati, jakadun kasashenwaje da kuma mutanen kasar ta Iran daga bangaorin daban daban, wadanda suka je gidansa don gaisuwar Salla karama.

Sayyeed Aliyul Khaminae, ya kara da cewa a cikin fiki'hun addinin musulunci, a cikin dukkan mazhabobin musulmi, hukuncin jihadidon kwatar kasar musulmi wacce kafirai ko makiyan musulmi suka kwace wajibi ne, a kan daddaikun al-ummar musulmi. Banda haka jihadin za'a yi shi ta hanya da ta sawwaka ga kowa don ganin kasar musulmi bata ci gaba da zama karkashin kafirai ba. Wannan hukuncin a fili yake.

Amma wasu kasashen musulmi a yau, abin mamaki da kuma ban hauci, suna daukar matsalar al-ummar Palasdinu, a matsayin wani abu marasamuhimmanci.

Banda haka, wasu kasashen Larabawa da musulmi a halin da mukeciki, suna ganin matsalar Palasdinu da Palasdinawa, bai da muhimmancin da wasu musulmi suke daukarsa.Amma gaskiyan lamarin wannan matsalar ita ce matsala mafi muhimmancia cikin al-ummar musulmi a yau. Sannan yin watsi da itsa ko kuma maida shi wani abu marsa muhimmanci ba dai dai ba ne.

An kafa haramtzcciyar kasar Israela ce a shekara ta 1948 M, bayan wani shirin da kasar Ingila wacce ta mamaye kasar Palasdinu bayan yankin duniya na daya. Sannan sakataren harkokin wajen kasar ta Ingila na lokacin "Arthur James Balfour" ya bayyana shirin kasarsa na samarwa yahudawan sahyoniyya kasar a kan kasar Palasdinu, Daga nan ne dubban yahudawa suka yi ta hijira zuwa kasar Palasdinu, sun ci gaba da korar Palasdinwa daga kasarsu suna kuma kashe su, har zuwa yanzu, inda Paladinawa kimani miliyon 6 ne yahudawa suka kora daga kasarsu suke kuma rayuwa mafi tsanana a kasashen daban daban na duniya. Banda haka wadanda suka rage a cikin kasar, a duk ranar Allahyahudawa suna kisan su.

A irin wannan halin, ba zai yu ba, musulmi mai imani ya yi shiru, ya kuma yi watsi da wannan matsalar ba, ko kuma ya manta da ita kamar babu wani abu da ya hau kansa ba.

Sai dai wasu kasashen Larabawa musamman kasar saudia, banda ma rashin daukin wannan matsalar a bakin kome, tana ma kara kusantar HKI don neman yerdarta.

A cikin yan makonnin da suka gabata, yerimai mai jiran gado sarautar kasar ta Saudia, Mohammad bin Salman, kafin a amince masa ya zama yerimai mai jiran gado, sai da ji kasar HKI sau da dama, yana haduwa da jami'an gwamnatin haramtacciyar kasar, yana kuma shaida masu cewa zai yi aiki tare da su, zai kuma taimaka wajen tabbatar da amincen kasar Israela.

Jaridar Haarez ta haramtacciyar kasar ta rubuta a cikin labaran ta kan cewa Mohammad bin Salman dan sarki salman kuma yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudia ya na zuwa kasar ta saudia tun shekara ta 2015 don tattauna wannan matsalar tare da su.

Don daka, a irin wannan halin, jagoran juyin juya halin musulci ya kammala da cewa akwai butunhadin kai mai karfi tsakanin al-ummar musulmi, da kuma aiki tare don sanya matsalar al-ummar Palasdinu a matsayin matsala mafi muhimmaci a tsakaninsu, kuma dole ne mu raya ita wannan matsalar cikin al-umma musumi, don yahudawan kansu suna yin duka abinda zasu yi don rarraba kan al-ummar musulmi ta hanyoyi da dama.

3613295


captcha