IQNA

Wani Babban Shago Ya Nemi Uzuri Daga Musulmi A Jamus

23:58 - June 28, 2017
Lambar Labari: 3481651
Bangaren kasa da kasa, wani babban shagon sayar da kayyaki na kasar Jamus ya nemi uzuri daga musulmi bayan nuna wani abinci ya kunshi naman alade a matsayin abincin halal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, nashara ta 324 da karamin ofishin jakadancin Iran ke fitarwa ta yi ishara da cewa, jaridar Hafington Post ta bayar da rahoton cewa, wannan shago ya nuna wani abinci mai suna nidl wanda ya kunshi naman alade a matsayin abincin halal da musulmi za su iya saye domin amfani da shi.

Wannan lamari ya bakanta ran musulmia kasar ta Jamus matuka, inda suka isar da wannan batu ga magabata na kasar, amma daga bisani bayan gudanar da bincike an gane cewa kamfanin yay i kure ne, domin kuwa akwai musulmi suna sayen abincin halal a wurin tsawon lokaci ba tare da an taba samun irin hakan ba.

Kamfanin dai ya fitar da sanarwa, wadda a ciki yake neman gafara daga dukkanin musulmi na kasar jamus baki daya, tare da shan alwashin ganin cewa hakan ba ta sake faruwa ba.

Musulmia kasar Jamus dai suna yin sayayye ne a mafi yawan lokuta a shaguna da ke karkashin kamfanoni masu kawo abincin halal daga kasashen larabawa da kuam kasashen gabashin nahiyar asia.

3613749


captcha