IQNA

Jiragen Yakin Isra’ila Sun Kai Hari A Gaza/Martanin Hamas

23:59 - June 28, 2017
Lambar Labari: 3481652
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hari a kan wasu yankuna acikin yankin zirin gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, da jijjifin safiyar jiya jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi lugudan wuta a kan wasu yankuna na Gaza.

Daga cikin wuraren jiragen yahudawan suka kai wa hari har wani wurin tsaro da ke karkashin bangaren mayakan Izzuddini Qassam bangaren soji na kungiyar Hamas.

A nata bangaren kungiyar ta hamas ta mayar da martani kan lamarin, da ke tabbatar da cewa hakika haramtacciyar kasar Isra’ila tana da wani boyayyen shiri na tsikanar Palastinawa domin bude wani sabon yaki a kan al’ummar Gaza.

Bayanin na hamas ya ce Palastinawa ‘yan gwagwarma suna nan a cikin shiri a kowane lokaci domin mayar da martani da dukkanin karfinsu a kan haramtacciyar kasar Isr’ila a duk lokacin da ta yi wani shishigi a kan al’ummar yankin na Gaza.

3613577


captcha