IQNA

An Yi Allah Wadai Da Harin Charlottesville / Gazawar Trump

22:13 - August 13, 2017
Lambar Labari: 3481794
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da jerin gwano wanda ya hada msuulmi da wadanda ba musulmi ba a garin Charlottesville na jahar Virginia a kasar Amurka domin yi Allah wadai da harin nuna wariya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, wannan jerin gwano na lumana ya samu halartar bangarorin da suka hada da na musulmi da kuma wadanda ba musulmi gami da bakake da faren fata.

Babbar manufar gudar da gangamin da kuma jerin gwanon ita ce yin Allah wadai da wani harin ta'addanci da wasu masu tsananin kyamar baki da nuna wariyar launin fata suka kaddamar a kan mutane a garin na Charlottesville, inda suka kasha mutum daya da kuma jikkata wasu 26 na daban.

A lokacin gudanar da wannan zanga-zangar dai an yi ta rera taken yin Allah wadai da salon siyasar Donald Trump tare da dora alhakin dukkanin irin wadannan muggan ayyuka a kan salon siyasarsa ta nuna wariya ga wasu jinsi a kasar.

Da dama daga cikin mahalarta wannan gangamin dai ba musulmi ba ne, amma musulmi ne suka kira jerin gwanon, domin nuna goyon bayansu ga sauran al'ummomi da ake nuna wa wariya da kuma danne musu hakkokinsu na dimukradiyya a kasar.

Kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna wajen nuna wariya da banbanci na launin fata da kuma addini a tarihi, amma amma daga baya lamarin ya lafa, sai dai kuma bayan hawan Donald Trumpa kan kujerar shugaban kasar kyamar baki da nuna wariya atsakanin al'ummar kasar ya sake dawowa kuma yana ci gaba da yin muni, kasantuwar gwamnatin kasar a halin yanzu ta doru ne a kan wannan salo.

3629750


captcha