IQNA

Taro Mai Taken Bayyanar Hadisi Madogarar Ilimi A Alkahira

23:27 - August 16, 2017
Lambar Labari: 3481804
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken bayyanar hadisi madogarar ilmomi a birnin Alkahira na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ideo-cairo cewa, wannan taro zai mayar da hankali a kan irin gudunmawar ilimin hadisi a cikin karni na hudu zuwa na twakwas hijira kamariyya, wati karni na goma zuwa na sha hudu hijira miladiyya.

Cibiyar gudanar da binciken ilimomi ta Dominican da ke birnin Alkahira ita ce ta dauki naushirwa da kuma gudanar da taron, wanda za a yi nan da watannihudu masu zuwa, tare da halartar masana daga ciki da wajen kasar.

Babban abin da taron zai mayar da hankali a kans dais hi ne, yadda a ckin wadannan karnoni hudu malaman hadisi suka mike tsaye wajen fitar da hadisai da kuma tace su gwargwadon iko, yin amfani da su a matsayin babban abin dogaro wajen fitar da ilmomin addinin musulunci, da hakan ya hada da fikihu, tafsiri, likitanci, falsafah, kalam da kuma sufanci.

Malami sun mayar da hankali matuka wajen sanin madogarar hadisi da kuma yin amfani da wannan damar wajen kokarin ganin an tantance ilmomi na addini ta hanyar hadisan da aka samu, maimakon yadda aka hana yin amfani da hadisi bayan rasuwar manzon Allah har zuwa wani lokaci.

A kan wannan ne cibiyar za ta kirkiro wata mujalla mai suna MIDEO, wadda za a fara bugawa a cikin shekara ta 2019, wadda za ta mayar da hankali kan wannan shiri.

3631109


captcha