IQNA

Cibiyar Musulmin Amurka:

Ku Hukunta Wanda Ya Ci zarafin manzon Allah (SAW)

21:56 - August 17, 2017
Lambar Labari: 3481807
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulmin kasar Amurka ta bukaci da a hukunta wani mutum da ya ci zarafin manzon Allah (SAW) a jahar Minnesota.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na «duluthnewstribune» ya bayar da rahoton cewa, wani mutum mai suna Joseph Frankis ya ci zarafin wani musulmi mai sayar da kayan ganye dan asalin kasar Somalia, kamar yadda ya jefe shi da naman alade da kuma yin kalaman batunci ga manzon Allah (SAW) da kuma msuulmi.

Majalisar musulmin kasar Amurka ta bukaci mahukunta a jahar ta Minnesota da su dauki matakin kama shi da kuma hukunta bisa abin da ya aikata, wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokokin kasar Amurka.

Jama'a da dama ne dai suka sheda abin da mutumin ya aikata, daga cikinsu kuwa har da wani dan sanda, wanda ya bayar da sheda akan cewa lallai mutumin ya ci zarafin musulmi.

Yanzu haka dai kotun jahar Minnesota na shirin gurfanar da wannan mutum domin hukunta a shi a kan laifin cin zarafin dam adam bisa banbancin addini da akida.

Cibiyar musulmin Amurka ta bayar da rahoton cewa, kyamar musulmi a cikin Amurka ta karu da kashi 91 cikin dari a cikin 2017, idan aka kwatanta da shekara ta 2016 da ta gabata.

3631528


captcha