IQNA

Azhar Ta Shiya Gasar Bincike Kan Hakkokin Mata A Cikin Kur’ani

20:44 - October 13, 2017
Lambar Labari: 3481996
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar muslunci ta kasar masar wato Azhar ta shirya gudanar da wata gasar bincike kan hakkokin mata a cikin kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na azhar.eg cewa, rubutun gasar zai kasance ne a cikin harsunan turancin ingilishi da kuma larabci, wanda za agudanar tare da hadin gwaiwa da bankin muslunci.

Gasar tana da sharuddan da aka gindaya, daga ciki akwai wadanda sun shafi mauduin rubutun kan cewa dole ne abin da za a rubuta ya zama cikin abin da mauduin gasar ya kunsa, kuma kada yawan shafukan ya zama kasa da shafi 100 kuma kada ya zama sama da shafuka 200.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa tana da matukar muhimmanci, kasantuwar wannan shi ne karon farko da ake gudanar da ita a kan wannan maudui wanda ya shafi hakkokin mata zalla a cikin kur’ani mai tsarki.

An saka kyautar kudu da za su kai fan 55,000 ga mutane 23 na farko da suka fi nuna kwazoa cikin wannan gasa, wadda za a kammala karbar dukkanin abubuwan da aka rubuta a cikin shekara mai kamawa.

3652144


captcha