IQNA

Ana Ci Gaba Da Dauki Ba Dadi Tsakanin palastinawa Da Yahudawa

20:54 - December 12, 2017
Lambar Labari: 3482195
Bangaren kasa da kasa, Ana ci gaba da gumurzu mai tsanani tsakanin Palasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yau tsawon kwanaki ke nan ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin al'immar Palasdinu da suke yankunan gabar yammacin kogin Jordan da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sakamakon matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Wani sabon gumurzun ya kunno kai a safiyar yau Talata musamman a garuruwan Bait-Laham, Baitu-Uyun da Khalil, inda Palasdinawan suka ja daga tare da hana sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila samun damar kutsawa zuwa cikin yankunan na Palasdinawa.

A daya bangaren kuma A zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a jiya Litinin wasu jakadun kasashen Larabawa sun fitar da daftarin kuduri kan neman tsoma bakin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da babban zauren Majalisar dangane da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da maida ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin lamarin da ya yi hannun riga da kudurorin majalisar Dinkin Duniya masu yawa.

Tun a ranar Laraba 6 ga wannan wata na Disamba ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kunnen uwar shegu ga dukkanin kiraye-kirayen da duniya suke masa na nisantar shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, inda ya yi gaban kansa tare da bada umurnin maida ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin na Qudus.  

3671921

 

captcha