IQNA

Sakon Jagora Kan Jerin Gwanon Ranar 22 Ga Bahman:

Al’ummar Iran Azamarku Ta Bada Wa Makiya Kasa A Fuska

23:42 - February 11, 2018
Lambar Labari: 3482385
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jijina wa al’ummar kasar Iran dangane da fitowar da suka yi a fadin kasar domin tabbatar wa duniya da cewa suna nan kan bakansu na riko da juyin musulunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, jagoran ya fitar da bayani dangane da taruka da jerin gwanon tunawa da juyin juya halin musulunci a fdin kasar.

Ga Matanin Sakon Kamar Haka:

Da Sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai

Al’ummar Iran mai girma, hakika a yau da azamarku da basirarku kun tabbatarwa duniya da matsayinku, domin fitowarku a yau domin nuna goyon bayanku ga juyin Islama ta fi ta kowane lokaci a tarihi.

Hakika wannan babban jawabi ne kuak bayar ga makiya da ‘yan koransu. Ko shakka babu makiya sun babban shiri na karya zukatan al’ummar Iran dangane da fitowa domin tunawa da zagayowar ranar juyi, ta hanyar yada farfaganda da kirkiro bayanai na karya domin karya zukatan jama’a, amma abin da kuka a yau ya tabbatar da gazawar makiya da ‘yan koransu, kuma kun tabbatar da cewa ku masu cika alkawali ne ga marigayi Imam, wanda ya jagoranci juyi domin, inda kuka yi ta rera taken nuna goyon bayanku ga daular musulunci da kuma kiran da marigayi Imam yay i.

Wannan tsayin daka da kuka nuna, ya rusa shirin da makiya suka kwashe shekaru suna yi, a yau sun gane cewa lallai duk abin da suka yi, sun tafka babban kuren lissafi, kuma za su ci gaba da gane kurensu sakamakon azamarku da basirarku.

Yana da kyau dukkanin jami’an gwamnati su kara azama domin ci gaba da raya wannan matsaya da al’umma ta dauka, haka nan kuma jami’ai su kara himma da azama wajen yin hidima ga al’umma domin wanzuwar juyin Islama, da kuma kare manufofinsa.

 

Kada Ku Raunana Kuma Kada Ku Yi Bakin Ciki Ku Ne Madaukaka In Kun Kasance Masu Sani

Wassalamu Alaikum wa rahmatullah

11 / 2 / 2018

3690706

 

captcha