Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na safa daga Palastinu ya bayar da rahoton cewa, wasu mutae da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kan masallacin tarihi a garin Gabisiyya da ke cikin lardin Jalil tare da gina wasu ramu a cikin masallacin.
Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa, mutanen sun shiga wurin ne da dare dauke kulake da karafa, ba a san ko suwane suka aikata hakan ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ma a gari safad inda hubbaen annabi Yusha (AS) magajin annabi Musa (AS) yake, an ci zarafin wasu Palstinawa mazauna gain gasibiyya, lamarin da ya fusata su matuka.
Haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya tana daukar matakan takurawa ga palastinawa da suke zaunea cikin yankunan da ta mamaye, tare da kafa musu dokoki da kaidoji na muzgunawa.