IQNA

An Kashe Khashoggi A Cikin Karamin Ofishin Jakadancin Saudiyya

23:51 - October 07, 2018
Lambar Labari: 3483031
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiya suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyya mai sukar gwamnati na nuni da cewa, an kashe shi ne a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar Turkiya sun bayar da tabbacin cewa Jamal Khashoggi bai fita daga karamin ofishin jakadancin Saudiyya ba, tun bayan da ya shiga cikin ofishin a ranar Talata da ta gabata.

A nasu bangaren kuma jami'an 'yan sandan kasar Turkiya masu gudanar da binciken kwakwaf kan batun sun sanar da cewa, sakamakon farko na bincikensu na nuni da cewa an kashe Khashogi a cikin karamin ofishin jakadancin an Saudiyya da ke Istanbul tun a ranar Talata da ta gabata.

Sai dai Saudiyya ta kore cewa tana da masaniya kan makomarsa, amma ta amsa cewa ya ziyarci ofishin nata a ranar Talata domin karbar wasu takardu, kuma ya fita bayan wani lokaci.

Jamal Khashoggi dai fitaccen dan jarida nea  kasar Saudiyya, wanda kuma ya yi ayyuka da manyan cibiyoyi a kasar, amma daga bisani ya rika sukar salon siyasar yarima Bin Salman, kamar yadda yake sukar yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan kasar Yemen.

3753403

 

 

captcha