IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Sudan

23:45 - December 03, 2018
Lambar Labari: 3483176
Bangaren kasa da kasa, a ranar Litinin mai zuwa ce zaa fara gudanar da gasar kur’ani ta kasa da kasa a birnin Khartum na kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ali Zain Mabruk Mabruk babban darakta mai kula da ayyukan shirya gasar kur’ani a Sudan ya bayyana cewa, sun kammala dukkanin shirinda ya kamata domin daukar nauyin bakuncin gasar.

Ya ce nnan gasa dai za ta samu halartar makaranta da maharta 60 daga kasashen duniya daban-daban, inda za su fara karawa da juna daga ranar litinin mai zuwa har tsawon mako guda.

Wannan gasar dai it ace karo na goma da ake gudanar da ita, kuma  awannan karon za ta shafi bangarori daban-daban da suka hada da harda, kira’a da kuma tafsiri, kamar yadda kumaza a yi la’akari da sanin hukuncin karatu.

Muhammad Rasul Takbiri mahardacin kur’ani mai tsarki daga kasar Iran, shi nezai wakilci akasar a wanna gasa.

3768862

 

 

 

captcha