IQNA

Guterres Ya Yi Gargadi Kan Karuwar Kyamar Musulmi A Duniya

23:53 - December 08, 2018
Lambar Labari: 3483197
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio ya nuna damuwa kan yadda ayyukan nuna kyama ga musulmi ke karuwa a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labaran Arab 48 ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron majalisar dinkin duniya na tunawa da cika shekaru 70 da amincewa da daftrin kare hakkokin bil adama a majalisar, Antonio Guterres ya bayyana cewa, abin bakin ciki ne yadda ake nuna wa musulmi banbanci a  wasu bangarori na duniya.

Ya ce ya damu matuka dangane da irin mawuyacin halin da aka jefa musulin Rohingya  a kasar Myanmar, wanda  a cewarsa dole ne a kawo karshen irin wanann mu'amala da ake yi wa musulmia  wasu kasashe.

Haka na kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi ishara da cin zarafin da aka yi wa mata 'yan kabilar Izid a kasar Iraki, inda 'yan ta'addan Daesh suke yi musu fyade da cin mutuncinsu a matsayin bayi ribatattun yaki, da kuma yadd a wasu kasashen nuna kyama ake yi ga muuslmi saboda addininsu, wanda ya ce dole ne a yi yaki da wannan dabi'a a duniya.

An gabatar da wannan daftarin kudiri ga majalisar dinkin duniya bayan gama yakin duniya na biyu, kuma an amince da shi a ranar 9 ga watan Disamban 1948.

3770368

 

 

 

 

 

captcha