IQNA

Bukukuwan Cika Shekara Guda da Murkushe Daesh A Iraki

19:47 - December 09, 2018
Lambar Labari: 3483201
Bangaren kasa da kasa, Gwamantin kasar Iraki ta sanar da cewa, a gobe Litinin a dukkanin fadin kasar za a gudanar da bukukuwan cika shekara guda da murkushe kungiyar 'yan ta'addan wahabiyawa ta Daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Al-khalij ya bayar da rahoton cewa, gwamantin kasar ta sanar da cewa, a gobe Litinin a dukkanin fadin kasar za a gudanar da bukukuwan cika shekara guda da murkushe kungiyar 'yan ta'addan wahabiyawa ta Daesh tare da kammala dawo da dukkanin yankunan da kungiyar ta kwace iko da su a lokutan baya a cikin kasar ta Iraki.

Daga cikin abubuwan da za a gudanar akwai jawabin da Firayi ministan kasar ta Iraki Adel Abdulmahdi zai gabatar ga al'ummar kasar, wanda dukkanin gidajen talabijin da radiyo na kasar za su watsa, bayan nan kuma za a girmama iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ta'addancin Daesh a kasar, kamar yadda kuma za a daga tutocin Irakia  dukkanin sassan kasar, da hakan ya hada da gidajen jama'a da wuraren kasuwanci da tituna da kan ababen hawa.

Kafin wanna lokacin dai gwamnatin Iraki ta sanar da wannan rana a matsayin rana hutu a kasar baki daya.

3770662

 

 

 

 

 

captcha