IQNA

Masar Za Ta Dauki Bakuncin Babban Taron Masana Musulmi Na Duniya

8:31 - December 11, 2018
Lambar Labari: 3483206
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar Azhar da ke kasar Masar ta sanar da cewa, nan ba da jimawa ba za a gudanar da babban taron kasa da kasa masana musulmi a babban mazaunin cibiyar da ke birnin Alkahira.

Masar Za Ta Dauki Bakuncin Babban Taron Masana Musulmi Na DuniyaKamfanin dillancin labaran iqna, hafin yada labarai na Al-ahram ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ciboyar ta Azhar ta fitar ta bayyana cewa, taron zai kunshi bangarori daban-daban na malaman addinin muslunci, da kuma masana masu nazari.

Babbar manufar taron dai ita ce yin nazari kan lamurra da suka shafi ilimi, da kuma duba irin gudunmawar da musulmi za su iya bayarwa wajen ci gaban al'ummomi a wannan zamani.

Baya ga haka kuma taron zai duba wasu daga cikin matsalolin da suke ci wa al'ummar musulmi tuwo a kwarya, musamman wadanda suke da alaka da banbancin mahanga da fahimta, inda za a gabatar da kasidu kan yadda musulmi za su hadu kan yin aiki guda bisa mahanga ta bai daya wadda addinin muslunci ya hada su a kanta.

Haka nan kuma taron zai duba kalu balen da ke gaban muuslmi na gurbata fahimtar akidar musulunci a tsakanin musulmi, wanda hakan ya haifar da akidu na ta'addanci, da yadda za a yi maganin hakan. Kamar yadda kuma taron zai duba hanyoyin da ya kamata musulmi su kara karfafa alakarsu da sauran bangarori da baa na musulmi ba, domin karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a duniya.

3770898

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar masar
captcha