IQNA

Azhar Na Shirin Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Duniya

23:22 - December 12, 2018
Lambar Labari: 3483209
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar musulunci ta Azhar akasar Masar ta sanar da cewa, tana da shirin gudanar da wata gasar kurani ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na almesryoo cewa, Abbas Shoman shugaban kwamitin manyan malaman Azhar ya bayyana cewa, cibiyar musulunci ta Azhar tana da shirin gudanar da wata gasar kurani ta duniya wadda za ta shafi hardar kur'ani zalla.

Ya ce wanann shiri zai kunshi bangarori daban-daban na hardar kur'ani mai tsarki, kuma gasar za ta kunshi fitattun mahardata ne na duniya wadanda suka samu kyautuka na kasa da kasa.

Shomjan ya kara da cewa, yanzu haka malaman cibiyar sun fara tattauna yadda gasar za ta kasance, da kuma abubuwan da za a tsara kafin gudanar da ita, da kuma wadanda za su zama alkalai daga kasashen da za a gayyace su.

Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai kamar yadda ya ambata, ita ce kara fadada lamarin kur'ani mai tsarki a cikin duniyar musulmi.

3771376

 

captcha