IQNA

Matsayar ‘Yar Majalisar Amurka Kan Lamurran Da Suka Saba Kaida

22:52 - March 13, 2019
Lambar Labari: 3483454
Tashar talabijin ta kasar Amurka ta nisanta kanta daga wani furuci da wata ma;aiakciyar tashar ta yi da ke cin zarafin 'yar majalisar dokokin Amurka musulma saboda saka lullubi da take yi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, tashar ta Fox News ta bayyana furucin ma'aikaciyar da cewa ra'ayinta ne na kashin kanta, amma ba ra'ayin tashar ne ba.

Ma'ikaciyar tashar ta Fox News ta yi kakkausar suka kan yadda 'yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Umar take shiga cikin majalisar da lullubi irin na addinin musulunci a kanta, inda ta bayyana hakan da cewa ya sabawa dokokin Amurka.

Wannan dai na daga cikin irin kalamai na tsangwama da Ilhan Umar take fuskanta daga bangarori daban-daban na masu adawa da ita a cikin kasar at Amurka, musamman kasantuwarta bakar fata kuma musulma.

3797601

 

 

captcha