IQNA

An Cafke Wani Matashi Da Yayi Barazana Kai Wa Musulmi Hari A Australia

23:34 - March 22, 2019
Lambar Labari: 3483481
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Ausralia sun cafke wani matashi dan asalin kasa bayan da yay i barazanar kawa musulmi hari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Qods Al-arabi cewa, jami’an tsaron kasar Ausralia sun cafke wani matashi dan asalin kasa bayan da yay i barazanar kawa musulmi hari a cikin masallaci tare da kashe su.

Yaron wanda ya fito daga jahar Victoria ya yi wannan barazana ne a cikin shafin sadarwa na yanar gizo, inda ya bayyana kin jinin muslunci da muuslmi.

Jami’an ‘yan sandan sun yaron bai wuce shekaru 14 da hahihuwa ba, a kan haka an sake a matsayin belin har zuwa ranar da za a kawo shi kotu.

Wannan na zuwa ne bayan mako guda da kai harin da yay i sanadiyyar yin shahadar masallata kimanin 50 a wani harin da aka kai musu a masallacia  kasae New Zealand.

3799317

 

 

captcha