IQNA

Taron Karatun Kur’ani Tare Da Halartar Mansur Karimi A Ghana

22:57 - May 19, 2019
Lambar Labari: 3483654
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron karatun kur’ani mai tsarki a jami’ar musulunci da ke kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar taron karatun kur’ani mai tsarki a babar jami’ar musulunci ta kasar Ghana, da ke birnin Accara fadar mulkin kasar, tare da halaratr bababn makarancin kur’ani mai tsarki sheikh Karim Mansuri da kasar Iran.

Taron dai dai ana gudanjar da shi a kowace shekara, inda akan gayyaci malamai da makaranta daga ciki da wajen kasar ta Ghana, inda akan gabatar da karatun kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma dalibai da suke karatu a jami’ar makaranta kur’ani daga cikinsu sukan gabatar da karatu da ma wasu shirye-shirye na daban da suka danganci addini a wajen taron, kamar yadda malamai sukan gabatar da kasidunsua  wurin.

Baya ga malamai,a kan gayyaci jami’an gwamnati, da kuma wakilan cibiyoyi na ilimi a kasar, inda jami’oi kantura wakilansu, da kuam sauran bangarori na kasa, domin samun wakilcia  wannan babban taro an kur’ani mai tsarki.

A wannan karo fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki Mansur karimi ne daga kasar Iran ya samu halartar wurin domin gabatar da tilawar kur’ani mai tsarki da Karin tangimi wanda aka fi saninsa da shi, inda ya samu kyakkyawar tarba daga daliban jami’a da suke shirya wanann babban  taro.

3812659

 

محفل انس با قرآن با حضور کریم منصوری در غنا + عکس

محفل انس با قرآن با حضور کریم منصوری در غنا + عکس

محفل انس با قرآن با حضور کریم منصوری در غنا + عکس

محفل انس با قرآن با حضور کریم منصوری در غنا + عکس

 

captcha