IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Ta Duniya A Morocco

23:35 - October 25, 2019
Lambar Labari: 3484190
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar kur’ani ta duniya karo na 15 a ranar Lahadi 27 ga Oktoba a kasar Morocco.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Alsharq ta kasar Qatar cewa, za a gudanar da wanann gasar karatun kur’ani ne ta duniya a birnin Kazablanka, tare da halartar wakilai daga kasashen duniya.

Wannan gasa dai za ta mayar da hankali ne a bangarorin harda da kuma tafsiri, musamman tafsirin izhi na 57, 58, 59, 60, da kuma ma’anonin kalmomi usamman wadanda suke da ma’ana ta balaga, haka nan kuma akwai harda da kuma tajwidi daga dukkanin bangarorin kur’ani, daga farkonsa har zuwa karshensa.

Cibiyar kula da harkokin addini ta Irshad daga kasar Qatar ita ce za ta dauki nauyin gasar baki daya, inda wakilin cibiyar Abdulaziz Abdullah Alhummari zai halarci wurin, kamar yadda shi ma zai yi karatun kur’ani na tartili a wurin gasar.

 

3852320

 

 

captcha