IQNA

Twitter Ta Taimaka Wajen Cin Zarain ‘Yan majalisa Musulmi A Amurka

23:07 - November 06, 2019
Lambar Labari: 3484227
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani bincike ya nuna cewa twitter ta taimaka wajen cin zarafin ‘yan majalisa musulmi a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Washington Post ta bayar da rahoton cewa, sakamakon wani bincike da aka gudanar kan sakonnnin cin zarafi dubu 113 da aka aike wa ‘yan majalisar dokoki Amurka musulmi ya nuna cewa, dukkanin sakonnin an aika da su ta hanyar twitter.

Bayanin ya ce mafi yawan abin da sakonsa dai shi ne cin zarafi da tuhumar ‘yan majalisar musulmi da cewa su ‘yan ta’adda saboda su musulmi ne, kamar yadda kuma mafi yawan sakonnin an fi tura su ga Ilhan Omar.

Jonathan Olbrait wani masanin harkokin zamantakewa a jami’ar Columbia ya bayyana cewa, kamfanin na twitter shi ne wanda ya sawwaka hanyoyin da mutane za su yi wannan cin zarafi da gangan, domin da kamfanin ya ga dama da haka ba ta faru ba.

3855126

 

captcha