IQNA

Jagoran Ansarullah Ya Yi Gargadi Kan Ci Gaba Da Kaiwa Yemen Hari

23:18 - November 10, 2019
Lambar Labari: 3484238
Bnagaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Ansarullah a Yemen ya gargadi Saudiyya kan ci gaba da kai hari kan kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babban saktaren kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce daga fara yakin kasar zuwa yanzu sama da gangar danyan man fetir miliyan 120 ne kawancen saudiya da hadaddiyar daular larabawa suka sace a yankunan da suka mamaye.

Sayyid Abdul-Malik Badreddin al-Houthi babban saktaren kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen a jiya asabar yayin da yake gabatar da jawabin barka da salla na murnar zagayowar ranar haifuwar fiyeyyen halitta manzon Allah (s.a.w.a) ya ce ci gaba da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar kasar da kawancen saudiya ke kaiwa zai fuskanci martani mai tsanani.

Al-Houthi ya ce ci gaba da killace kasar ya bawa masanar kasar damar ci gaba a kere-kere na bangaren harakokin tsaro, kuma duk wadanda suke bayan yaki su san cewa daga karshen za su kwashi hasara mai yawa.

har ila yau, babban saktaren kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya tabbatar da cewa daga lokacin fara yakin Yemen zuwa yanzu sama da gangar danyan man fetir miliyan 120 ne kawancen saudiya da hadaddiyar daular larabawa suka sace a yankunan da suke mamaye da su.

3855773

 

captcha