Shafin yada labarai na dar-alquran.org ya bayar da rahoton cewa, A;li Hadi Kazem daraktan cibiyar kula da harkokin kur'ani a hubbaren Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa, a halin yanzu mahardata kur'ani mai tsarki 500 ne ke halartar gasar kur'ani ta kasar Iraki da aka fara gudanarwa karkashin kulawar cibiyar.
Ya ce tun a ranar Laraba da ta gabata ce aka fara gudanar da gasar, kuma har yanzu ana cikin mataki na farko ne, kafin zuwa mataki na gaba.
Mahalartan sun fito ne daga jihohi 12 na kasar ta Iraki, kuma an kafa kwamiti karkashin hubbaren Imam Hussain (AS) wanda shi ne yake kula tare da daukar nauyin dukkanin abin da ya shafi wannan gasa ta kur'ani.