IQNA

Wasu Falastinawa Sun Daga Tutocin Iran Da Falastinu A Masallacin Quds

14:30 - June 08, 2021
Lambar Labari: 3485992
Tehran (IQNA) wasu daga cikin Falastinawa masu fafutuka sun daga tutocin Iran da Falastinu a cikin harabar masallacin Quds mai alfarma.

Tashar al'alam ta bayar da rahoton cewa, a jiya wasu daga cikin Falastinawa masu fafutuka sun daga tutocin Iran da Falastinu a cikin harabar masallacin Quds mai alfarma, domin nuna godiya dangane da matakin da kasar ta Iran ta dauka na taimaka ma al'ummar Falastinu tsawon shekaru, a daidai lokacin da duniya ta yi watsi da su.

Masu fafutukar sun nuna godiya kan goyon baya da taimakon da Iran ta yi musu a cikin kwanakin da Isra'ila ta dauka tana kaddamar da hari a kan a baya-bayan nan.

Bayan kawo karshen hare-haren Isra'ila a kan yankin zirin gaza a 'yan makonnin da suka gabata, shugaban kungiyar Hamas Isma'ila Haniyya ya bayyana cewa, Iran ce ta taimaka musu da kudi da kuma makaman kariyar kai da mayar da martani a kan hare-haren Isra'ila.

Tun kafin wanann lokacin tsawon shekaru fiye da ashirin, marigayi janar Qasem Sulaimani ne yake shigar  da makamai zuwa ga kungiyoyin Falastinawa ;yan gwagwarmaya a yankin zirin Gaza, tare da ba su horo na soji.

اهتزاز پرچم ایران در صحن‌های مسجد الاقصی و مسجد صخره + عکس و فیلم

اهتزاز پرچم ایران در صحن‌های مسجد الاقصی و مسجد صخره + عکس و فیلم

 

3976119

 

captcha