IQNA

An Yi Gargadi Kan Yiwuwar Sake Farfadowar Kungiyar ‘Yan Ta’addan Daesh Masu Da’awar Jihadi

14:46 - June 10, 2021
Lambar Labari: 3486001
Tehran (IQNA) bangaren kula da bin diddigin lamurran musulmi a  duniya na cibiyar Azhar ya yi gargadin yiwuwar sake farfadowar ‘yan ta’addan Daesh masu da’awar jihadi.

Shafin jaridar Al-ahram ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, rahoton karshe da bangaren kula da bin diddigin lamurran musulmi a  duniya na cibiyar Azhar ya harhada kan makomar Daesh, ya yi ishara da  yiwuwar sake farfadowar ‘yan ta’addan na Daesh.

Rahoton ya ce, tun bayan da ‘yan ta’addan suka sha kashi a kasar Syria tare da karya lagonsu a shekara ta 2019, daga lokacin zuwa yanzu sun himmatu da yukurin sake samar da wasu mayaka wadanda za su yi amfani da su domin ci gaba da ayyukan ta’addanci a cikin Syria da ma sauran kasashen duniya.

Haka nan kuma rahoton ya yi bayanin cewa, a yanzu Daesh na kokarin hada mayaka dubu 27, wadanda dukkaninsu matasa ne majiya karfi, daga cikinsu akwai ‘ya’yan wasu ‘yan ta’addan da aka halaka a kasar Syria, da kuma wasu daga wasu kasashe da suke da magoya baya.

Baya ga kasashe larabawa, akwai dubban ‘yan ta’addan Daesh da suka fito daga kasashen turai daban-daban, wadanda akasarinsu an hakala su a Syria, kuam da dama daga cikinsu iyalansu na nan a sansanonin da aka tsugunnar da sua  waus yankuna na Syria, inda mayakan da ke samun goyon bayan Amurka ko Turkiya ne suke kula da su.

Kungiyar tarayyar turai ta bayyana amincewarta da wannan rahoto da bangaren kula da bin diddigin lamurran musulmi a  duniya na cibiyar Azhar ya harhada kan makomar Daesh, da kuma yiwuwar sake farfadowar kungiyar.

3976558

 

 

 

captcha