IQNA

Kasar Finland Ta Fara Raba Wa 'Yan Wasa Mata Musulmi Mayafin Kai

23:02 - June 17, 2021
Lambar Labari: 3486022
Tehran (IQNA) Finland ta raba kyallen yin lullubi a lokacin wasa domin su samu natsuwa kamar yadda addininsu ya yi uamrni.

Rahotanni daga kasar Finland sun ce, hukumar wasannin kwallon kafa ta kasar ta raba kyallen yin lullubi a lokacin wasa domin su samu natsuwa kamar yadda addininsu ya yi umari.

Hukumar wasannin kwallon kafa ta kasar Finland ta samar da 'yan kwalaye masu yawa, domin mata musulmi masu sh'awar yin kwallon kafa.

Wannan mataki ya zo ne sakamakon yadda 'yan wasa mata da suka kware wadanda kuma musulmi ne ba su shiga cikin wasannin, saboda ba a ba su damar saka lullubia  kansu, wanda kuma kasar tana da bukatarsu a wannan fage saboda kwarewarsu.

Heda Plaga ita ce shugabar hukumar kwallon kafa ta mata a kasar Finland, ta bayyana cewa dukkanin musulmi da suke wasannin kwallon kafa a kasar za su iya saka lullubia  kansu a lokacin wasa indai suna bukatar yin hakan.

Akasarin musulmin kasar Finland dai baki ne daga kasashen larabawa ko kasashen Afirka, ko kasashen nahiyar asia.

3977955

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: lullubi kyalle wasannin natsuwa
captcha