IQNA

Shugabannin Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Aike Wa Zababben Shugaban Iran Da Sakonnin Taya Murna

16:10 - June 20, 2021
Lambar Labari: 3486030
Tehran (IQNA) Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da taya Ebrahim Ra’isi murna akan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Iran.

Sakonnin baya-baya nan su ne shugabannin kasashen da suka hada da, Nicolas Maduro, na Venezuela da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, da babban shugaban kwamitin sulhu na Afghanistan Abdullah Abdullah, duk sun taya Ebrahim Raisi murna akan nasarar zaben da akayi masa.

A cikin sakonsa, Mahmud Abbas ya jaddada bukatar ci gaba da hadin kai tsakanin bangarorin biyu ‘yan’uwa juna, inji shi.

"Muna fatan cewa tare da nasarar Raisi, alakar da ke tsakanin gwamnatocin biyu da al'ummomin biyu a fannonin al'adu da tattalin arziki, yaki da fataucin muggan kwayoyi, ta'addanci za a kara fadada ta tare," in ji Shugaban Hukumar Kula da Sulhu ta Kasar Afghanistan, Abdullah Abdullah.

"Za mu ci gaba da aiki tare don samar da zaman lafiya da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu," kamar yadda shi ma shugaba Maduro na Venezuella ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dama kafin zababen shugaban kasar ta Iran, Ibrahim Ra’isi, ya samu sakon taya murna daga shugaban kasar Rasha, da na Turkiyya da kuma na Siriya Qatar Kuwait da dai sauransu.

Shi ma dai shugaban kungiyar Hezbollah, ta kasar Lebanon, Hassan Nasrullah, ya taya Ibrahim Raisin Murna, ta hanyar sakon da ya aike a shafinsa na tuwita.

 

3978787

 

 

 

 

 

 

 

captcha