IQNA

Kayayyakin Abincin Halal Na Kasashen Musulmi Na Samun Karbuwa A Afirka Ta Kudu

16:54 - December 07, 2021
Lambar Labari: 3486653
Tehran (IQNA) Kamfanonin da ke samar da kayayyakin abincin halal sun yaba da irin karbuwar da kayansu ke samu a kasar Afirka ta kudu.

A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, kamfanonin da suke samar da kayayyakin abincin halal sun, bayyana cewa a cikin shekarun baya-bayan nan kayansu na kara samun karbuwa cikin sauri a kasar Afirka ta kudu.
 
Wannan yana zuwa ne dai a daidai lokacin da harkokin yawon bude a nahiyar Afirka ke kara bunkasa, wanda kuma kasar Afirka ta kudu na daya daga cikin kasashen da ke samun miliyoyin masu yawon bude daga ko’ina cikin fadin duniya a kowace shekara.
 
Rahoton ya ce, daya daga cikin abubuwan da musulmi masu yawon bude a kasashen duniya suke fuskantar matsala a kansa shi ne abincin halal, musamman a kasashen da ba na musulmi ba, amma samun wuraren kayan halal a kasashe masu samun ‘yan yawon bude daga kasashen duniya, zai ja hankulan musulmi masu sha’awar yawo zuwa wadannan kasashen, wanda kuma shi ne babban abin da Afirka kudu ta yi la’akari da shi.
 
Baya ga haka kuma, abincin halal da kamfanonin kasashen larabawa da na musulmi suke samarwa, yana samun kwastomomi har da wadanda ba musumi ba, kasantuwar cewa abinci ne mai kyau ta fuskar lafiya.
 
Baya ga kasar Afirka ta kudu, yanzu haka wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka da suke samun masu yawon bude ido daga kasashen duniya, sun fara mayar da hankali wajen samar da abincin halal, domin jawo hankalin msuulmi masu yawon bude zuwa kasashensu.
 

4017117

 

captcha