IQNA

Al'ummar kasar Jordan sun yi watsi da matakin gwamnati na takaia ayyukan cibiyoyin haddar kur'ani

15:04 - June 17, 2022
Lambar Labari: 3487431
Tehran (IQNA) Masu fafutuka a kasar Jordan sun kaddamar da wani gangami a shafukan sada zumunta domin nuna adawa da matakin da gwamnati ta dauka na hana cibiyoyin haddar kur'ani mai tsarki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Joe 24 cewa, masu fafutuka a kasar Jordan sun kaddamar da wani gangami a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana rashin amincewarsu da sharuddan da gwamnatin kasar ta gindaya kan cibiyoyin haddar kur’ani mai tsarki da kuma cibiyoyin muslunci a kasar.

Daya daga cikin wadannan sharudda shi ne rage lokutan aiki na cibiyoyin kur’ani da kuma sanya sharuddan gudanar da su da kuma gudanar da jarrabawar malamai daga ma’aikatar da ke kula da wa’aqa da harkokin addinin Musulunci.

Masu fafutuka da na kusa da kungiyoyi da cibiyoyi na Musulunci suna ganin wadannan sharudda ba za su taba yiwuwa ba idan aka yi la’akari da yanayin kungiyoyin da ake ganin na sa kai ne kuma suke taka rawa wajen ilmantar da matasa da haddar kur’ani mai tsarki.

Hassan al-Riyati dan majalisar dokokin kasar Jordan ya ce tsarin da ma'aikatar kula da harkokin addini  ta kafa wanda majalisar ministocin kasar ta amince da shi a baya-bayan nan, ya takaita ayyukan kungiyoyi na haddar kur'ani mai tsarki bisa sharuddan da aka gindaya a cikinsa.

4064516

 

 

 

 

captcha