IQNA

Dole Ne kan Saudiyyah Ta Yi Bayani / Bisa Dokoki Na Kasa Da Kasa

22:37 - October 01, 2015
Lambar Labari: 3377208
Bangaren siyasa, Dr Hassan rauhani ya bayyana gwamnatin Saudiyya da cewa it ace take da alhakin dukkanin abin da ya faru kuma dole ne su amince da cewa laifinsu, domin kokarin dora wa wasu alhakin hakan shi ne babban abin da ke kara tabbatar da rashin gaskiyarta a cikin wannan lamari na kisan mahajjata.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nbakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shugaban kasa kan tattaunawarsu da Christian Ammanpour, cewa, shugaban ya yi ishara a cikin kalamansa da ke tabbatar da cewa, hakika rashin cancantar daukar dawainiyar gudanar da ayyukan hajji da matakin sakaci da ko-in kula gami da rashin aiki da hakkin da ya rataya a kan mahukuntan Saudiyya sune musabbabin faruwar hatsarin Mina da ya kai ga hasarar dubban rayukan mahajjata aikin hajjin bana da suka fito daga sassa daban daban na duniya.

Bayan shudewar kwanaki shida da faruwar hatsarin Mina, dalilai da hujjoji da suke tabbatar da sakaci, halin ko in kula da rashin aiki da hakkin da ya rataya a wuyar mahukuntan Saudiyya wajen gudanar da ayyukan hajji suna kara bayyana a fili duk da matakan farafaganda da yada labarun karya marassa tushe da mahukuntan Saudiyya da 'yan korensu ke yi a sassa daban daban na duniya.



A matakin farko, gidan sarautar Saudiyya ya yi kokarin rufe matsalar hatsarin Mina tare da bayyana cewa wata karamar matsala ce da ta saba aukuwa a lokacin aikin hajji ta turereniya da rashin hakurin mahajjata amma bayan da yawan mahajjatan da suka rasa rayukansu yake ci gaba da karuwa, hakan ya tilastawa mahukuntan Saudiyya canza baki tare da daukan matakin boye hakikanin abin da ya janyo hatsarin musamman ganin yadda kasashen musulmi suka fito fili suna bayyana tsananin damuwarsu kan batun.



Shugaban ma'aikatar da ke kula da aikin hajji da ziyara a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sa'id Auhidi ya bayyana cewa; A halin yanzu haka dai suna da tabbacin rasuwar mahajjatan kasar Iran 239 tare da jikkatan wasu 14 na daban gami da matsalar bacewar mahajjata dari biyu da arbain da daya lamarin da ke fayyace cewa matsalar hatsarin Mina ya wuce haddin yadda ake yadawa a kafafen watsa labaran mahukuntan Saudiyya da masu kare musu manufofi ido rufe a sassan duniya.



A jawabinsa ga manema labarai a filin jirgin Mihr Abod da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a jiya Talata bayan katse zaman tattaunawa da wakilan kasashen duniya daban daban a gefe bayan taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya; Shugaban kasar Iran  shugaban na Iran  ya jaddada cewa; Rashin kula da nuna halin ko-oho gami da rashin daukan matakan da suka dace; sune suka janyo hasarar rayukan mahajjatan bana a Mina.



Yana mai fayyace cewa; A mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran lallai akwai rina a kaba dangane da abin da ya faru a Mina, sakamakon haka ya zame dole a kan mahukuntan Saudiyya su yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu a karkashin dokokin kasa da kasa tare da fayyace wa duniya hakikanin abin da ya janyo faruwar wannan hatsari.

A nashi bangaren kakakin gwamnatin Iran Muhammad Baqir Noubakhti ya yi furuci da cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata mika batun matsalar Mina zuwa gaban hukumomin kasa da kasa domin bin bahasin lamarin sakamakon matakin da mahukuntan Saudiyya suka dauka na neman wofantar da matsalar tare da rashin mutunta gwamnatocin kasashen da mahajjatansu suka rasa rayukansu.



Noubakhti ya kara da cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zata taba amincewa da batun neman bisine mahajjatan Iran a kasar Saudiyya ba, don haka dole ne a kan mahukuntan na Saudiyya su hanzarta mikawa kasar Iran gawawwakin mahajjatanta tare da fayyace hakikanin musabbabin faruwar wannan hatsari mai tada hankali a filin Mina.



A gefe guda kuma ministan lafiya na kasar Iran Hasan Qadi Zade Hashimi a halin yanzu haka yana ci gaba da gudanar da ziyarar aiki a kasar Saudiyya domin ganawa da mahukuntan kasar da nufin tattauna batun hanyar dawo da dukkanin Iraniyawa da suka rasa rayukansu a hatsarin Mina zuwa ga iyalansu tare da ganawa da tawagar likitocin Iran da suke kula da lafiyar mahajjatan kasar a lokacin aikin hajji gami da zagaya asibitocin da aka kwantar da Iraniyawan da hatsarin na Mina ya ritsa da su domin duba lafiyarsu.



3375925

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha